Romans 1

1Wasiƙa daga Bulus, bawan Kiristi Yesu, kirayaye yǎ zama manzo keɓaɓɓe kuma domin bisharar Allah—  2bisharar da Allah ya yi alkawari tuntuni ta bakin annabawansa a cikin Nassosi Masu Tsarki 3game da Ɗansa, wanda bisa ga mutuntakarsa zuriyar Dawuda ne, 4wanda bisa ga Ruhun tsarki, aka shaida shi da iko cewa shi Ɗan Allah ta wurin tashinsa daga matattu. Wannan bishara kuwa game da Yesu Kiristi Ubangijinmu ne. 5Ta wurinsa da kuma saboda sunansa, muka sami alheri muka kuma zama manzanni don mu kira mutane daga cikin dukan Alʼummai zuwa ga biyayyar da take zuwa daga bangaskiya. 6Ku ma kuna cikin waɗanda aka kira ku zama na Yesu Kiristi.

7Wannan wasiƙa ce zuwa ga dukanku da kuke a Roma waɗanda Allah yake ƙauna, waɗanda kuma ya kira domin su zama tsarkaka:

Alheri da salama gare ku daga Allah Ubanmu da kuma daga Ubangiji Yesu Kiristi.

Marmarin Bulus Ya Ziyarci Roma

8Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a koʼina a duniya. 9Allah, wanda nake bauta wa da dukan zuciyata cikin waʼazin bisharar Ɗansa, shi ne shaidata a kan yadda kullum ina tunawa da ku 10cikin adduʼoʼina a kowane lokaci; ina kuma adduʼa cewa a ƙarshe in Allah ya yarda hanya za ta buɗe mini in zo wurinku.

11Ina marmarin ganinku don in ba ku wata baiwar ruhaniya, don ku yi ƙarfi—  12wato, don ni da ku mu ƙarfafa juna ta wurin bangaskiyarmu. 13Ina so ku sani ʼyanʼuwa cewa na yi shirin zuwa wurinku sau da dama, amma aka hana ni yin haka sai yanzu. Na so in zo domin in sami mutane wa Kiristi a cikinku, kamar yadda na yi a cikin sauran Alʼummai.

14Ina da hakki ga Helenawa da waɗanda ba Helenawa ba, ga masu hikima da kuma marasa azanci. 15Shi ya sa na yi himma sosai in yi muku waʼazin bishara ku ma da kuke a Roma.

16Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata: da farko ga Yahudawa, saʼan nan ga Alʼummai. 17Gama a cikin bishara an bayyana adalci daga Allah wanda yake ta wurin bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”
Hab 2.4


Fushin Allah a kan ʼYan Adam

18Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa-madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa-ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.

21Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. 22Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.

24Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen shaʼawace shaʼawacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. 25Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci-wanda ake yabo har abada. Amin.

26Saboda wannan, Allah ya yashe su ga shaʼawace-shaʼawacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ʼyanʼuwansu mata wadda ba daidai ba. 27Haka ma maza suka bar alʼadar kwana da mata suka tunzura cikin shaʼawar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.

28Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba. 29Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne, 30da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girmankai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu; 31su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi. 32Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.

Copyright information for HauSRK